An Zabi Tebboune A Matsayin Shugaban Aljeriya A Karo Na 2

Algeria holds presidential election

Shugaban hukumar ANIE Muhammad Charfi ya shaidawa manema labarai cewa fiye da mutane milyan 5.3 ne suka zabi Tebboune, kwatankwacin kaso 94.56 cikin 100 na kuri’un da aka kada a zaben.

A jiya Lahadi, hukumar zaben Aljeriya (ANIE) ta bayyana cewa an sake zaben shugaban kasar mai ci Abdelmadjid Tebboune da kusan kaso 95 cikin 100 na kuri’un da aka kada.

Shugaban hukumar ANIE Muhammad Charfi ya shaidawa manema labarai cewa fiye da mutane milyan 5.3 ne suka zabi Tebboune, kwatankwacin kaso 94.56 cikin 100 na kuri’un da aka kada a zaben.

Tebboune mai shekaru 78 ya samu rinjayen goyon bayan sake samun wa’adin mulki na 2 mai shekaru 5 akan abokin hamayarsa mai matsakaicin ra’ayin Islama Abdelaali Hassani mai shekaru 57, wanda ya samu kaso 3.17 cikin 100 na kuri’un da aka kada, da dan takara mai ra’ayin gurguzu Youcef Aouchiche dan shekara 41 wanda ya samu kaso 2.16 na kuri’un.

Fiye da al’ummar Aljeriya miliyan 24 suka yi rijistar zabe, sai dai ANIE ba ta bayyana adadin mutanen da suka kada kuri’a a zaben da ya gudana a Asabar din da ta gabata ba.