A yau Alhamis, Shugaban China Xi Jinping ya dauki alkawarin tallafawa Afirka da fiye da dala biliyan 50 nan da shekaru 3 masu zuwa, inda ya sha alwashin yaukaka alaka da kasashen nahiyar a bangaren samar da kayayyakin more rayuwa da cinikayya yayin da yake jawabi a taro mafi girma da birnin Beijing ya karbi bakunci tun bayan annobar Korona.
A jawabinsa ga shugabannin yayin kaddamar da taron a birnin Beijing, Shugaba Xi ya yabawa kawancen kasar da Afirka.
Xi ya kara da cewa, “a shirye China take ta kyautata alaka da kasashen Afirka a fannonin masana’antu da noma da samar da kayayyakin more rayuwa da cinikayya da kuma zuba jari.
“Nan da shekaru 3 masu zuwa, gwamnatin China nada niyar bayar da tallafin kudaden da suka kai yuan biliyan 360 (kwatankwacin dala biliyan 50.7).
A cewar Shugaba Xi, za a bada fiye da rabin adadin kudaden a matsayin bashi, inda za a zuba dala biliyan 11 “cikin nau’ukan tallafi daban-daban” sannan a bayar da dala biliyan 10 ta hanyar karfafa gwiwar kamfanonin China su zuba jari.
Ya kuma dauki alkawarin taimakawa wajen “samar da akalla guraben aikin yi miliyan daya a nahiyar Afirka”.
Shugaban na China ya kuma sha alwashin bada agajin dala miliyan 141 a matsayin tallafi ga hukumomin soji a nahiyar Afirka.
Dandalin Mu Tattauna