Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ZABEN GHANA: Hukumomi Za Su Yi Wa Jam'iyu Adalci


Shugaban Hukumar Zaben Kasar Ghana Bossman Asare
Shugaban Hukumar Zaben Kasar Ghana Bossman Asare

Hukumomi sun ba al'ummar kasar Ghana tabbacin cewa, za a yi wa dukan jam'iyu adalci a babban zaben da za a gudanar cikin watan Disamba, yayinda su ka kuma yi alkawarin ganin cewa, an gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali da luimana,

Shugaban kasar Ghana, Nana Addo Dankwa Akufo-Addo da Sufeto Janar din ‘yan sandan Ghana, Dokta George Akufo-Dampare, a wurare daban daban sun tabbatarwa ‘yan Ghana cewa, za su yi iya kokarinsu don ganin an gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali da lumana.

A wani taron manema labarai, Mataimakin Shugaban Hukumar Zabe, Dakta Bossman Asare, yayi watsi da ra’ayin cewa, alhakin tabbatar da zaman lafiya da sakamakon zabe ya rataya ne kawai a kan Shugaban Hukumar, kamar yadda ake tafka muhawara kan rawar da hukumar ke takawa wurin tabbatar da ingantaccen zabe cikin lumana.

Wasu jam’iyun siyasa sun koka, musamman babbar jam’iyar adawa ta NDC wacce ta bukaci a baiwa kamfanin bincike mai zaman kansa dama ya binciki rijistar ‘yan kasa da hukumar zabe ta gudanar, bisa hullar cewa, akwai kura-kurai da yawa da ka iya jawo magudi.

Manyan Jam'iyun kasar Ghana suna gabatar da manufofinsu
Manyan Jam'iyun kasar Ghana suna gabatar da manufofinsu

Sai dai jam’iyar NPP mai mulki na ganin a halin yanzu ba ta ga wata matsala daga hukumar zabe ba, domin hukuma ce mai zaman kanta, kuma ta yi tsarin yadda za ta tafiyar da harkokinta, ba jam’iyun siyasa ne za su nuna mata yadda za ta tafiyar da harkokinta ba.

A taron manema labarai da hukumar zabe ta shirya, ta mayar da martani dangane da zargin, kuma hukumar ta kare martabar rajistar masu kada kuri’a na shekarar 2024, kamar yadda mataimakin shugabar hukumar, Dokta Bossman Asare yace, “Muna kira ga jama’a da su yi watsi da kalaman cewa rajistar ba ta dace da zaben 2024 ba, ko kuma tana da kura-kurai. Rijistar tana da inganci, kuma rajistar da aka tabbatar a ƙarshe, zata fito ne da gyare-gyaren duk kurakurai da aka gano”.

Taron Kawancen Kungiyoyin Siyasa Da Za Su Kalubalanci Manyan Jam’iyyu A Zaben Ghana
Taron Kawancen Kungiyoyin Siyasa Da Za Su Kalubalanci Manyan Jam’iyyu A Zaben Ghana

Dakta Bossman Asare ya kara da cewa, Hukumar zaben ba ta da niyyar gurbata rijistar don baiwa wata jam’iyyar siyasa dama fiye da sauran jam’iyu.

A hirar shi da Muryar Amurka, Dokta Imurana Mohammed, darekta shirye-shirye na Hukumar wayar da kan jama’a NCCE, ya bayyana wasu kalubale da hukumarsa ke hangowa da illarsu idan ba a dakile su ba. Yace, “Na farko shi ne labaran da ake yadawa a yanar gizo da ba a san asalinsu ba. Na biyu shi ne, jamiyun adawa sun kalubalanci hukumar zabe … idan ba a duba an magance wannan kalubalen ba, zai iya kawo cece-kuce a wannan zaben”.

Masana na cewa lallai yana da muhimmanci, ga masu ruwa da tsaki, ciki har da jam’iyyun siyasa da ‘yan kasa, su yi aiki tare da hukumar zabe yadda za a tabbatar da an gudanar da zaben cikin lumana da sahihanci, yadda kasar za ta ci

gaba da taka muhimmiyar rawa a fagen dimokradiya a Afirka.

Saurari cikakken rahoton Idris Abdallah:

ZABEN GHANA: Hukumomi Za Su Yi Wa Jam'iyu Adalci
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:04 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG