Wannan Jumu'a ce cikar shekaru hamsin da biyar bayan kisan Firimiyan lardin Arewacin Najeriya, Sir Ahmadu Bello Sardauna da wasu shugabanni na wannan lokacin a juyin mulki na farko da soji suka yi a shekarar 1966.
Ana ci gaba da tunawa da Sardauna amma dai mutanen mahaifarsa da ke Sakkwato sun ce ba su gamsu da yadda aka sakawa masa ba akan hidimar da yayi wa al'umma.
Abubakar Yusuf, Dan Masanin Rabah, wanda ya yi magana da yawun Masarautar Rabah, mahaifar Sir Ahmadu Bello Sardauna, ya nuna yadda aka fita batun gidan na Firimiya, a maimakon a yi wani abu a mahaifarsa don nuna cewa da gaske ake.
Su ma dangin Sardauna dake zaune a garin har yanzu sun tofa albarkacin bakinsu kan sadaukarwar da yayi wa Najeriya. Sun nuna bukatar a nuna kaunar Sardauna ta wajen raya mahaifarsa.
Abubakar Bala Rabah, Yariman Rabah, shi ma Jigo ne kuma mazaunin garin na Rabah. A Rana irin wannan kungiyoyi sukan shirya taruka domin tunawa da sadaukarwa da Firimiya yayi wa yankin Arewa da Najeriya baki daya.
Zaidu Bala Kofa Sabuwa shi ne shugaban kungiyar muryar Talaka ta kasa wadda takan shirya irin wadannan tarukka a kowace shekara.
Yanzu dai shekaru 55 Sir Ahmadu Bello Sardauna baya duniya amma yanzu ana tuna shi, abinda wasu ke ganin bai rasa nasaba da gaskiya da adalci da yayi a lokacin shugabancinsa Wanda kuma abin koyi ne ga shugabannin wannan lokaci.
Ga Muhammad Nasir da cikakken rahoton:
Your browser doesn’t support HTML5
Karin bayani akan: Ahmadu Bello, Sardaunan Sakkwato, Nigeria, da Najeriya.