An Yi wa Neymar Tiyata A Gwiwa

Lokacin da Neymar ya ji raunin

A ranar Asabar ake sa ran za a sallami Neymar mai shekaru 31 daga asibiti.

An yi wa dan wasan Brazil Neymar aiki a gwiwarsa ta hagu a ranar Alhamis a cewar Kamfanin Dillancin Labarai na AP.

An yi wa dan wasan gaban na Brazil aikin ne a asibitin Belo Horizonte a cewar kafofin yada labaran cikin gida.

Bayanai sun yi nuni da cewa likitin kungiyar kwallon kafar ta Brazil ne ya yi wa Neymar tiyatar.

Sa’a hudu aka kwashe ana aikin a cewar jaridar yanar gizo ta Globo Esporte.

Dan shekaru 31, Neymar, wanda ake sa ran sallamarsa daga asibiti a ranar Asabar, ya ji raunin ne a karawar da Brazil ta sha kaye a hannun Uruguay a ranar 17 ga watan Oktoba da ci 2-0.

Wasan na neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya ne.