Shugaban ya kuma zargi tsofaffafin shugabanni hukumar binciken manya laifuka ta FBI da aikata laifin cin amanar kasa.
Bayan sanar da tallafi ga manoma, Trump ya maida martani a kan asarar da Amurka ke yi a kasuwancinta da China, yayin da yake amsa tambayoyi da wani rukunin ‘yan jarida kakilan.
Shugaba ya sha caccakar kakakin Majalissar wakilai Nancy Pelocy, wanda yace ta fadawa wakilin Amurka a harkokin kasuwanci Robert Lighthizer, cewa “tana bukatar makwanni biyu tayi nazarin yarjejeniyar cinikayya tsakanin Amurka da Canada da Mexico.
Trump, ya kira Pelosi “marar hankali, ba tayi nasara ba, kuma tana da matsaloli” ya kuma kwatanta shawarar Pelosi da abin “kazanta” inda take cewa, “ya kamata iyalan shugaban kasa su dauki mataki a kan halayensa.
Ya kuma kira kansa da cewa shi “kwararre ne ta kowane fanni”
Jim kadan, Pelosi ta maida martani a shafinta na Tweeter cewa. “a duk lokacin da mai kiran kansa kwararre ya fara nuna halayen shugaba, zanyi farin cikin aiki da shi a kan batutuwa da suka shafi ci gaban kasa.