Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Ci Gaba Da Zaman Doya Da Man Ja Tsakanin Majalisa Da Shugaba Trump


Shugaba Donald Trump
Shugaba Donald Trump

Fadar White House ta umarci tsohon Lauyarta kada ya bayyana a gaban Majalisar tarayya, kamar yadda ma’aikata Shari’a ta shawarta.

Dama yau ne Lauya Don McGahn, wanda ya samu sammacin daga kwamitin shari'a na majalisa, zai bayyana gaban kwamitin harkokin shari'a na majalisa da ya bukace shi ya je ya bada bahasi.

“Suna yin wannan ne domin kare ofishin shugaban ‘kasa domin shugabannin masu zuwa,” a cewar shugaban kasa Donald Trump da yake magana kan shawarar da ma’aikatar Shari’a ta bayar. Ya kara da cewa “ba wai suna yi domin ni bane.”

Trump ya yi maganar ne daga fadar White House kafin ya shiga jirginsa, inda daga nan zai nufi wani gangamin siyasa a Pennsylvania.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG