Hadarin ya hallaka alhazai fiye da dari daga wasu kasashen duniya.
Shaikh Tijjani Bala Kalarawi na cikin malaman da suka jagoranci addu'ar rahama ga wadanda suka rasu. Ya kira 'yanuwan wadanda suka mutu su yi farin cikin irin mutuwarsu saboda irinta ce Allah yake so, wato ya kira bawansa a wurin da suka rasu. Shi Allah ne zai yi masu masauki.
Maimakon a yi bakin cikin mutuwarsu sai a yi murna akan kyakyawar mutuwar da suka yi.
A nashi bangaren jagoran aikin hajin bana mai martaba sarkin Kano Sanusi Lamido yace lokaci ya kusa da za'a yi aikin haji ba tare da tallafin ko sisin kwabo daga gwamnatin tarayya ba. Yayi misali da sansanin alhazai na jihar Kano wanda yace ba da kudin gwamnati aka gina ba lokacin gwamnatin Audu Bako. Da kudin alhazan aka gina.
Dangane da matsayin da sarkin ya dauka na tsayawa a Minna har na tsawon kwana uku maimakon biyu sai yace ya yi hakan ne saboda a rage cinkoson jama'a wurin tashi zuwa gida. Yace shi da sauran shugabanni zasu zauna saboda da zara sun tashi kowa ma zai fice ya tafi tun kafin a bude filin jirgin sama jirage su soma tashi. Sai dai duk wanda yake da lallura sai a bari ya tafi.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya.
Your browser doesn’t support HTML5