An Yi Jana’izar Mataimakin Shugaban Kasar Malawi Da Ya Rasu A Hatsarin Jirgin Sama

Malawi - Jana'izar mataimakin shuganban kasar

An yi jana'izar mataimakin shugaban kasar Malawi, Saulos Chilima a kauyensa dake kudancin babban birnin kasar a yau Litinin.

Shugaban kasar Lazarus Chakwera ne ya jagoranci jana’izar inda ya yi kira da a gudanar da bincike don gano musabbabin faruwan hatsarin jirgin.

Malawi

Chilima da wasu mutane tara ne suka mutu a hatsarin a makon da ya gabata a yankin Mzimba na arewacin kasar ta Malawi.

An gudanar da jana'izar a babban filin wasa na Bingu Bingu da ke birnin Lilongwe ranar Lahadi, inda Chakwera da wasu manyan baki suka yi masa bankwanan karshe.

“Kokenmu akan neman sanin abin da ya jinkirta neman wannan jirgin ne. Ina so in tabbatar muku, 'yan Malawi, cewa wani kwararre mai zaman kansa ne zai binciki wannan hatsarin," in ji Chakwera yayin da jama'a suka yi ta ba'a.

Daruruwan sojoji da jami’an ‘yan sanda da masu kula da gandun daji sun shafe sama da sa’o’i 24 suna bincike kafin a gano tarkacen jirgin a wani dajin da ke kudancin Mzuzu.

Jirgin ya taso daga Lilongwe zuwa birnin Mzuzu da ke arewacin kasar a lokacin da ya bace da safiyar Litinin din da ta gabata.

Chakwera ya kara da cewa a baya masu kula da zirga-zirgar jiragen sama sun hana jirgin sauka saboda rashin kyawun yanayi, kuma jirgin ya koma Lilongwe. Daga nan ne hulda tsakanin jami’an kula da zirga-zirgar jiragen da jirgin ya yanke.

-AP