Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Malawi na Neman Wani Jirgin Sama Da Ya Bace Dauke Da Mataimakin Shugaban Kasar


Mataimakin shugaban kasar Malawi Saulos Chilima, da matarsa Mary
Mataimakin shugaban kasar Malawi Saulos Chilima, da matarsa Mary

Sojoji na duba tsaunuka da dazuzzuka da ke kusa da wani birni a arewacin Malawi bayan da wani jirgin saman soja dauke da mataimakin shugaban kasar ya bace a yankin a ranar Litinin, in ji shugaban kasar Lazarus Chakwera.

WASHINGTON, D. C. - Jirgin da ke dauke da mataimakin shugaban kasa Saulos Chilima dan shekaru 51 da haihuwa da kuma wasu mutane tara ya taso ne daga Lilongwe babban birnin kasar da ke kudancin nahiyar Afirka da karfe 9:17 na safe, kuma ya kamata ya sauka cikin mintuna 45 a filin jirgin saman Mzuzu na kasa da kasa, mai tazarar kilomita 370 daga arewacin kasar.

Shugaban kasar Malawai Lazarus Chakwera
Shugaban kasar Malawai Lazarus Chakwera

Amma jami’an kula da zirga-zirgar jiragen sama sun fada wa matukin jirgin cewa ya juya saboda rashin kyawun yanayi kuma ba a ganin hanya, in ji Chakwera a wani jawabi da ya yi wanda aka nuna kai tsaye ta talabijin din MBC mallakar gwamnatin kasar. Jim kadan bayan wannan sakon sai hanyoyin sadarwar jirgin suka bace daga na’urar da ke bibiyar sa, a cewar Chakwera.

“Na san wannan lamari ne mai tada hankali. Na san cewa muna fuskantar fargaba da damuwa. Ni ma na damu,” in ji Chakwera. "Amma ina so in tabbatar muku da cewa zan bi duk hanyar da ta dace don ganin an gano jirgin, kuma ina da kyakkawan fata za a gano wadanda suka tsira."

Mzuzu shi ne birni na uku mafi girma a kasar Malawi kuma babban birnin yankin arewacin kasar.

Shugaban ya sha alwashin cewa za a ci gaba da aikin nema da bincike har cikin dare. "Na ba da tsattsauran umarnin cewa a ci gaba da aikin har sai an gano jirgin," a cewar Chakwera.

Chakwera ya kuma ce Amurka, Birtaniyya, Norway da Isra'ila sun yi mishi tayin ba da taimako a aikin binciken.

-AP

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG