Kusan maza 30 da aka kashe aka yi wa yankar rago a harin, wanda aka fara ranar Asabar 28 ga watan Nuwamba da safe a kauyen Zabarmari da ke jihar Borno. Mazauna kauyen sun ce akalla mutane 70 ake kyautata zaton an kashe a harin, yayin da jami’an tsaro ke neman wasu da yawa da har yanzu ba a san inda suke ba.
Yayin da babu kungiyar da ta dauki alhakin kai harin, mayakan Boko Haram ko na ISWAP sun taba yin irin wannan kisan gillar a baya. Har yanzu su na gudanar da ayyukansu a yankin, inda mayakan suka kashe akalla mutane 30,000 cikin shekaru 10 da suka wuce.
Shugaba Muhammadu Buhari ya yi Allah wadai da harin ya kuma ce kasar baki daya ta ji zafin harin.
Wani mazaunin kauyen da kuma kungiyar kare hakkokin bil’adama ta Amnesty International sun ce har da mata 10 cikin wadanda suka bace.
Mazauna yankin Kwashobe a Zabarmari, sun bayyana wa Muryar Amurka cewa mutanen da harin ya shafa sun je aikin shinkafa ne a gona yayin da suka hadu da ‘yan ta’addar da da suka yi musu yankar rago. Sun kuma yi kira ga gwamnati da ta dauki matakan da suka dace don kawo karshen mayakan.
Gwamnan Jihar Borno, farfesa Babagana Umara Zulum ne ya jagoranci jana'izar a Zabarmari; ya kuma bayyana harin a matsayin abin takaici tare da jajanta wa al’ummar yankin, ya kuma ce gwamnati za ta yi iya kokarinta don ganin an shawo kan wannan lamari.
Saurari rahoton Haruna Dauda Biu:
Your browser doesn’t support HTML5
Your browser doesn’t support HTML5