An Yi Jana’izar Idriss Deby Yayin Da Makomar Chadi Ke Cike Da Rashin Tabbas

Your browser doesn’t support HTML5

An yi jana’izar Shugaban Chadi Idriss Deby Itno da aka kashe a N’Djamena, babban birnin kasar a ranar Juma’a.

An yi jana’izar Shugaban Chadi Idriss Deby Itno da aka kashe a N’Djamena, babban birnin kasar a ranar Juma’a.

Shugaban gwamnatin wucin gadi, Mahamat Idriss Deby, wanda da ne ga marigayin, ya jagoranci bikin jana’izar, wanda ya samu halartar shugabannin kasashen duniya. Marigayi Deby, wanda ya mulki kasar wacce ke tsakiyar Afirka, har tsawon shekara 30, ya rasu ne yana da shekara 68.

Deby, babban na hannun daman kasashen yammacin duniya ne a yaki da ake yi da masu ikrarin jihadi a Afirka, an ji masa mummunan rauni ne a wannan mako, yayin da ya kai wa dakarun kasar ziyarar a fagen yakin da suke yi da ‘yan tawaye a cewar kakakin rundunar sojin Chadi.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron, ya halarci taron jana’izar na ranar Juma’a tare da wasu fitattun shugabannin kasashen Afirka, da suka hada da Faure Gnassingbe na Togo, da Shugaba Mohamed Bazoum na Nijar.

Bayan an kammala jana’izar da addu’o’i a babban masallacin N’Djamena, an tafi da gawar Deby Amdjarass, wani kauye da ke da tazarar tafiyar kusan kilomita 1,000 (mil 621) daga babban birnin kasar domin a binne shi.

Yanzu haka makomar kasar ta Chadi na cike da rashin tabbas.

Shugabannin ‘yan adawa da ‘yan tawayen da ake zargi da kashe Deby, sun ce ba su ji dadi ba saboda a cewarsu, dora dansa Mahamat Idriss Deby mai shekara 37 da dakarun kasar suka yi akan karagar mulki don ya jagoranci gwamnatin wucin gadi, tamkar juyin mulki ne.