An Yi Girgizar Kasa A Kasar New Zealand

Wata girgizar kasa mai nauyin maki 5 da digo 7 ta girgiza birnin nan na Christchurch da ke kasar New Zealand, sai dai har zuwa yanzu ba wani rahoton da ya nuna wata gagarumar jikkata.

Bangaren sashen yanayin Amurka ya ruwaito cewa girgizar kasar ta taso ne daga gabashin birnin da kimanin kilomita 17 inda ta nutsa da kimanin kilomita 8.

Sai dai sun ce ba wata alamar gargadin guguwar Tsunami dake kadowa daga teku, wato irin guguwar nan da aka taba yi a shekarar 2011.

Har ma ta halaka akalla mutane 185 tare da tarwatsa duk taswirar tsakiyar birnin.

New Zealand dai na kan doron kasar da ke tsakanin teku wanda a ko wane lokaci ana iya ganin faruwar girgizar kasa a yanki. Da yake kasar na wani tsibiri ne mai kewaye da Teku.