Kimanin sama da shekaru 104 ke nan da suka wuce, wannan shahararren jirgin ruwa mai suna “Titanic” da ya nitse cikin teku. A wannan shekarar aka kera wannan jirgin don ‘yan yawon shakatawa. Shi dai jirgin ya hadu da hadari ne inda yayi karo da wata narkekiyar kankara a cikin tsakiyar teku. Hakan ya tadama mutane hankali da dama.
A lokacin hadarin kimanin sama da mutane 1,500 ne suka rasa rayukan su, wasu kuma da suka tsira sun jikkata. Hadarin jirgin ya zama wani abu da ya taba duniya baki daya. Saboda hakan yasa a shekarar 1997, akayi wani fim mai sunan jirgin “Titanic” da aka bayyanar da labarin yadda abun ya faru harzuwa karshe, duk daga taimakon wani daya daga cikin wadanda suka rayu bayan shekaru 80 da aukuwar abun.
Wani hamshakin mai kudi dan kasar Australia Mr. Clive Palmer, ya dauki nauyin gyara wannan jirgi, wanda za’a kawata shi da wasu abubuwan zamani, kuma za’a kayatar da shi da wasu na’urorin, kamar su abun hangen nesa, rigar ceton rai, za kuma a kara mishi fadi kadan da zai kai mita 4, da wajajen hutawa, da dai sauran abubuwa na zamani a karni na 21, wanda wancan jirgin a wancan lokacin bashi da. An bayyanar da cewar wannan jirgin mai suna “Titanic ll” za’a fara amfani da shine a shekarar 2018 idan Allah ya kaimu.