Akan sa sama da hotuna milliyan 360 a shafin facebook a kowace rana a duniya, akwai wasu hanyoyi da dama da mutun zai iya gujema yadda shafin facebook ke canza ma mutun hotuna batare da izinin su ba.
Abu na farko da ya kamata mutun ya sani shine, za’a iya tagin aboki a hoto, amma a hana sauran abokan shi ganin hoton, ma’ana shi wannan abokin kadai ake so yaga hoton. Don yin haka kuwa sai ayi tagin na mutun sai aje inda akace audience, sai aje sauran zabi sonka sai a danna Custom, daga nan sai a danna inda akace friends of tagged, daga nan abokin ka kadai zaiga irin hoton da kake so ya gani.
Wata sabuwar dama kuma da shafin ya samar itace “featured photos” ita dai wannan wata damace da mutun zai zabi wasu hotuna guda 5, na shi da zai sa su cikin runbun ajiyar shi, wanda a duk lokacin da wasu baki suka shiga shafin na shi wadannan hotunan su zasu bayyana ma mutane ko shi wanene. Duk hotunan da zasu fito a wannan gurin yana da kyau mutane su sani cewar kowa zai iya ganin wadannan hotunan.
Akwai bukatar mutane su san irin hotunan da zasu dinga sawa a shafufukan su, da kuma irin kyau da hotunan su kayi, haka da irin girman su, da bai gaza nauyin da ake kira pixels 851 zuwa 315, haka kada ayi amfani da hoton da ya gaza fadin pixels 160 da tsawo 160, a hoton da za'a daura, don yin hakan zai sa hotunan baza su bayyana ba.