Tuni dai aka mika shi zuwa kasarsa Uganda kuma ana tsare da shi a wani kurkukun sojoji dake birnin Kampala, kamar yadda matarsa ta bayyana a yau Laraba.
Kizza Besigye ya yi takara da shugaban Uganda Yoweri Museveni a zabubbuka hudu, kuma yayi rashin nasara a dukkaninsu, duk da cewar yana kin amincewa da sakamakon, yana zargin tafka magudi da razana masu zabe. An sha kama shi sau da dama a baya.
“Ina kira ga gwamnatin Uganda data gaggauta saki mijina Dr. Kizza Besigye daga inda ake tsare da shi,” a cewar matarsa Winnie Byanyima.
An kasa samun kakakin rundunar sajin Uganda domin yin sharhi akan batun nan take.
“A matsayinmu na ‘yan sanda bama rike da shi, don haka baza mu iya cewa komai ba,” kamar yadda aka ruwaito kakakin rundunar ‘yan sandan Uganda Kituuma Rusoke ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Reuters.
Shima kakakin rundunar ‘yan sandan Kenya bai yi martani kan bukatar tofa albarkacin bakinsa kan batun ba nan take.
-Reuters