Wacce a nan ne aka kashe dan uwansa. Netanyahu ya sauka a filin sauka da tashin jiragen sama na Entebbe, inda a nan ne dakarun Isra’ila suka taba cetar mutane fasinjoji 100 da ma’aikatan jirgin Air France da aka yi garkuwa da su ran 4 ga watan Yulin shekarar 1976.
Mutumin da sojojin suka sha wuya akan cetonsa amma abin bai yiwu ba shine Jonathan Netanyahu, wanda shine yayan Benjamin Netanyahu din. Bayan tambara bikin tunawa da wannan lamari, Netanyahu zai halarci wani taron shugabannin nahiyar game da matsalar tsaro.
An bukaci bada hadin kan kasashen Afirikan a Majalisar Dinkin Duniya, inda anan ne aka fi sukar lamirin Isra’ila na mamaye tekun gabar yammacin Turai da kulle yankin zirin Gaza.
Wannan goyon baya zai zama a matsayin musayar samun tallafi da taimakon yaki da ta’addanci. A karshe Netanyahu zai ziyarci Kenya da Ethiopia da Rwanda.