Mutumin da ya aikata wannan kisan gilla ta hanyar sare kan uban gidansa bayan daya satar masa kusan dala dubu 400, ya shaidawa alkalin yankin Manhattan cewa kamata ya kare rayuwarsa a gidan kaso.
A cewar jaridar New York Post, an yankewa, Tyrese Haspil, hukuncin zaman gidan kaso na shekaru 40 zuwa daurin rai-da-rai a shari’ar kisan kai da sare kan shugaban wani kamfanin fasaha, Fahim Saleh, da ta gudana a yankin Lower Eastside a shekarar 2020.
‘Yan sanda sun bayyana cewa Haspil yayi aiki karkashin Saleh a matsayin “mataimaki na musamman” kuma shine ke gudanar da harkokin kudi dana kashin kai na mai gidansa wanda ya kasance dan kasuwa mai hada-hada tsakanin kasa da kasa-kuma mai gidan nasa na binsa bashin “dimbin kudade.”
Bashin ya samo asali ne daga zargin wawure dala dubu 400 da Haspil yayi daga dukiyar mai gidansa Saleh, wanda ya kafa wani kamfanin bada hayar babura a Najeriya a shekarar 2018 mai suna “Gokada”, wanda a yanzu ya rikide zuwa kamfanin rarraba sakonni.