Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bai Kamata ‘Yan Najeriyar Da Aka Daure Kan Rashawa Su Ci Gajiyar Shirin Afuwar Gwamnati Ba - Fagbemi


Ministan Shari’ar Najeriya, Lateef Fagbemi, ya bayyana cewar bai kamata mutanen da kotu ta daure akan cin hanci da rashawa su ci gajiyar shirin yin afuwar gwamnati ba.

Da yake jawabi a jiya Litinin a yayin wani taron karawa juna sani da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC ta shiryawa kwamishinonin shari’a na jihohin Najeriya, Fagbemi yace zai bada shawara a taron gyaran kundin tsarin mulki na gaba cewar bai kamata duk wadanda aka taba samu da laifin cin hanci da rashawa su ci gajiyar alfarmar yafiya da afuwa ta gwamnati ba.

A cewar antoni janar na tarayyar, “zan bada shawara a taron gyaran kundin tsarin mulkinmu na gaba cewa a tsame wadanda aka samu da laifin cin almundahana daga cin gajiyar alfarmar yafiya da afuwar gwamnati”

Ya kuma jaddada mahimmancin hadin kai tsakanin dukkanin masu ruwa da tsaki, musamman masu rike da mukamin antoni janar, a yakin da ake yi da almundahana, inda ya bukace su da kada su bari kabilanci da bita da kullin siyasa da hamayya da bambancin addini suyi tasiri a ayyukansu.

Fagbemi ya kuma bukaci hukumomin yaki da almundahana dasu tabbatar sun gudanar da cikakken bincike akan zarge-zargen cin hanci da rashawa gabanin su gurfanar da wadanda ake zargi gaban kuliya domin kaucewa kace-nace a kafafen yada labarai.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG