Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nijar: Kotu Ta Umurci Mahukunta Su Gaggauta Baiwa Wasu Sabbin Jami’an Kwastam Damar Fara Aiki


Janar Abdouramane Tchiani
Janar Abdouramane Tchiani

Kotun daukaka kara ta birnin Yamai a Jamhuriyar Nijar ta umurci mahukunta su gaggauta baiwa wasu sabbin jami’an kwastam damar fara aiki kokuma a biya su diyyar miliyan 50 na cfa a kowace rana tsawon shekaru 5.

Matasa sama da 100 ne aka ayyana cewa sun yin nasara daga cikin wadanda suka rubuta jarabawar shiga aikin kwastam da gwamnatin Nijar ta shirya a shekarar 2018 sai dai bayan kammala daukan horo baiwa wadanan sabbin jami’ai dama su fara aiki ya ci tura.

Kawo yanzu hukumomi ba su bayyana matsayinsu ba dangane da wannan al’amari da suka gada daga shudeddiyar gwamnatin farar hula wanda kuma ko a wancan lokaci ba a taba fitowa fili aka bayyana ainihin dalilin turjiyar da ke tattare da batun shigar da wadanan sabbin jami’ai a sahun ma’aikata ba.

Sakataren hadaddiyar kungiyar kwadago ta CNT Mounkaila Halidou na cewa ya zama wajibi gwamnati ta bi umurnin kotu don kada a ja wa kasa asarar kudade.

Wani rukunin na daban na irin wadanan ma’aikata da ke kunshe da sabbin sufetocin ma’aikatar kwastam sama da 50 da suka ci jarabawa a shekarar 2020 na ci gaba da jira a ba su damar soma aiki bayan kammala daukan horo.

Su ma turjiyar da wancan rukuni ke fuskanta ita ce ta rutsa da su koda yake wasu na ganin yiwuwar za ta canza zane a bisa la’akari da manufofin gwamnatin mulkin soja ta CNSP.

A saurari cikakken rahoton Souley Moumouni Barma:

Nijar: Kotu Ta Umurci Mahukunta Su Gaggauta Baiwa Wasu Sabbin Jami’an Kwastam Damar Fara Aiki
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:56 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG