Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotu Ta Bada Belin Masu Zanga-Zangar Tsadar Rayuwa A Kan Naira Milyan 10 Kowanensu


Zanga-zangar Tsadar Rayuwa A Najeriya
Zanga-zangar Tsadar Rayuwa A Najeriya

kotun ta umarci kowane daga cikin wadanda ake tuhumar ya samar da mutum guda mazaunin Abuja da zai tsaya masa wanda a shirye yake ya mika mata fasfon tafiye-tafiyensa da kananan hotunansa guda 3.

Wata babbar kotun tarayya dake zamanta a abuja ta bada belin masu zanga-zangar tsadar rayuwa (ta endbadgovernance) dat a gudana tsakanin ranaikun 1 zuwa 4 ga watan agustar daya gabata, su 10 da aka tuhuma da yunkurin hambarar da gwamnatin shugaban Najeriya Bola Tinubu, akan naira miliyan 10 kowannensu.

Da yake yanke hukunci a kan bukatar bada belin, Mai Shari’a Emeka Nwite, yace wajibi ne masu zanga-zangar su gabatar da mutanen da zasu tsaya musu wadanda dole ne ya kasance sun mallaki gida ko fili a Abuja kuma su mika takardun kadarorin ga kotu.

Haka kuma kotun ta umarci kowane daga cikin wadanda ake tuhumar ya samar da mutum guda mazaunin Abuja da zai tsaya masa wanda a shirye yake ya mika mata fasfon tafiye-tafiyensa da kananan hotunansa guda 3.

Yayin da yake fatali da korafin babban sufeton ‘yan Najeriya akan bukatar bada belin wadanda ake tuhumar, Mai Shari’a Nwite ya kuma umarci su da kada su sake shiga wani gangamin jama’a tsawon lokacin da suke fuskantar shari’a.

Haka kuma alkalin ya bada umarnin cigaba da tsare mutanen a gidan kaso har sai sun kammala cika sharudan bada belinsu.

Ana zargin mutanen ne da aikata laifin cin amanar kasa yayin zanga-zangar gama-garin mako guda sa’ilin da aka zarge su da ayyana yaki akan Najeriya.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG