Littafin da aka rubuta dangane da shugabancin Trump, da wani dan jarida da ake dorawa alhakin sauke shugaba Richard Nixon daga karagar mulki, ya bayyana gwamnati mai ci a matsayin wadda take neman kifar da kanta da kanta, da kuma rudani cikin watanni goma sha tara na farko da kafa gwamnatin.
Littafin da ake kira “Tsoro: Shugaba Trump a fadar White House, mai shafi dari hudu da arba’in da takwas, da Bob Woodward ya rubuta,wanda za a fitar ranar goma sha daya ga wannan watan na Satumba, ya bayyana cewa, mataimakan shugaban kasa suna satar takardun bayanai a kan teburinsa da kuma daukar wadansu matakai da nufin yiwa shugaban kasa yankan baya.
Littafin ya bayyana Trump a matsayin wanda bai san abinda ke faruwa a kasashen duniya ba, da kuma fadar dake cike da kurakurai da kuma mummunan rashin jituwa tsakanin mukarraban shugaban kasa.
A sakon da ya buga a shafinsa na twitter jiya Talata da yamma, shugaba Trump ya kuma nemi sanin ko Woodward sojan hayar jam’iyar Democrat ne.