An Tuhumi Tsohon Shugaban Yakin Neman Zaben Trump Da Cutar Amurka

Hukumomi a Amurka sun tuhumi tsohon shugaban yakin neman zabe na shugaba Donald Trump, Paul Manafort, a yau litinjin da laifin hada baki don cutar Amurka, da batar da sawun kudaden haramun, da kuma yin karya ga gwamnati a wani yunkurin neman gatanci ga tsohon shugaban kasar Ukraine.

Mai bincike na musamman dake bin sawun katsalandar da kasar Rasha ta yi a zaben shugaban kasa na 2016 a Amurka, Robert Mueller, shine ya tuhumi Manafort da wani abokin huldar kasuwancinsa, Rick Gates, a wani bangaren binciken da yake gudanarwa.

Sune mutanen farko da Mueller ya tuhuma a wannan bincike da yayi watanni 5 da farawa, koda yake tuhumar ba ta da alaka kai tsaye da zaben.

Manafort da Gates, sun mika kawunansu ga Hukumar Binciken Manyan Laifuffuka ta Tarayya a birnin Washington, inda ake sa ran nan bada jimawa ba za a gabatar da su a gaban kotun tarayya.

Shugaba Trump, ya sha bayyana binciken da Mueller, ke yi da kuma wani wanda majalisar dokoki ke gudanarwa game da alakar dake tsakanin kwamitin yakin neman zabensa da kasar Rasha a zaman bi-ta-da-kullin da ‘yan jam'iyyar Democrat ke amfani domin kafa hujjar kayen da yayi ma tsohuwar sakatariyar harkokin waje Hillary Clinton a zaben shugaban kasa.

Amma Mueller, tsohon daraktan Hukumar Binciken Manyan Laifuffuka ta Tarayya ce wanda akasari a nan Washington ake dauka a zaman mutumin da ba sh da wani ra’ayi na siyasa.