Sa’oi kafin a zo karshen wa’adin da shara’a ta yanka kafin a sako dimbin bayanan dake bada karin haske kan kisan gillar da akayi wa tsohon shugaban Amurka, John F. Kennedy, shugaban Amurka din na yanzu Donald Trump yace gwamnatuinsa zata ci gaba da rike daruruwan bayanan asiri dangane da wannan kisan, akalla na wani lokacin wucingadi.
A bayanan da suka baiwa manema labarai shekaranjiya Laraba, jami’ai sunce nan take, bada bata lokaci ba, Hukumar Tanadin Kayan Tarihi ta Amurka zata bankado takardu kamar 2,800 masu alaka da tarihin kisan.
Galibin takardun dai duk suna maida hankali ne kan tafiyarda Lee Harvey Oswald, mutumen da ya kashe shugaban yayi ne zuwa kasar Mexico, wattani biyu kafin zuwan shugaba Kennedy birnin Dallas a ran 22 ga watan Nuwamban 1963, ranar da aka kashe shi.
Facebook Forum