Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Limaman Yahudanci da Kiristanci Na Amurka Sun Roki Israila Ta Daina Sayar wa Kasar Myanmar Makamai


Mata Musulmai 'yan Rohingya da MDD ta ce kasar Myanmar na yi masu kisan gilla
Mata Musulmai 'yan Rohingya da MDD ta ce kasar Myanmar na yi masu kisan gilla

Limaman Yahudanci da Kiristanci su 300 na Amurka sun roki Israila ta daina sayar wa kasar Myanmar makamai saboda Majalisar Dinkin Duniya ta ce tana yiwa 'yan kabilar Rohingya Musulmai kisan kar dangi

Limaman Yahudanci da Kiristoci kamar 300 na Amurka sun aika wani rubutaccen sako ga hukumomin kasar Isra’ila, suna rokonsu da cewa su daina saida makamai ga gwamnatin kasar Myanmar, wacce Majalisar Dinkin Duniya, MDD ta ce tana yi wa ‘yan kabilar Rohingya Musulmi kisan kare dangi.

A cikin rokon da suka yi jiya Alhamis, marubutan sunce: “A matsayinmu na Amurkawa kuma Yahudawa, ba zamu taba goyon bayan Amurka ko Isra’ila su rinka bada horaswa ko makamai ga duk wata rundunar sojan da ta dukufa wajen anfani da matakan rashin Imani na ganin bayan wata al’umma mai karamin karfi ba.”

Haka kuma limaman sunce a yanzu ma suna iya maimaita lafazin nan na cewa “Har Abada Ba Za’a Sake Ba”, wanda suke anfani da shi duk lokacinda suke tuna abinda ya sami Yahudawa a hannun shugabannin Jamus ‘yan Nazi masu ra’ayin kyamar akidar Yahudanci.

Sai dai ma’aikatar harakokin wajen Isra’ila tayi anfani da lafazi mai gauni wajen musanta cewa tana da hannu a tashin hankalin dake faruwa a can Myanmar, koda yake kuma wani kusar gwamnatin ta Isra’ila yace gwamantinsu zata yi abinda ya kira “sabon nazari” akan makaman da take saidawa Myanmar din.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG