An tuhumi shugaban ‘yan adawan kasar Zimbabwe, Tendai Biti, da laifin tunzura jama’a wajen ta da husuma da kuma ayyana sakamakon zaben shugaban kasar mai cike rudani ba bisa ka’ida ba, wanda aka yi a makon da ya gabata.
Yayin da ya isa kotu a Harare, babban birnin kasar ta Zimbabwe, Biti wanda tsohon ministan kudi ne ya ce, “za su ci gaba da fafutuka.”
An maido da Biti gida daga kasar Zambia mai makwabtaka da Zimbabwen, inda ya je neman mafaka, bayan da hukumomin Zambian suka ki amincewa da bukatarsa ta zama a kasar.
A wani labari na daban kuma, wata sabuwar jam’iyyar adawa a Afrika ta Kudu, ta nemi gwamnatin kasar ta kori dukkan bakin da ke zaune kasar, tana mai ikrarin cewa, sune suke aikata laifuka tare da haifar da matsalar rashin aikin yi.
Duk da cewa jam’iyyar, wacce ake kira African Basic Movement, ba ta da tagomashin da za ta samu gagarumar nasara a zaben gama-gari da ke tafe a shekara mai zuwa, bullar jam’iyyar, a cewar masu fashin baki, alama ce da ke nuna cewa guguwar masu son madafun ikon siyasa su koma hannu jama’ar da ake mulka, ta isa kasar ta Afirka ta Kudu.