Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Zimbabwe Ba Zai Kafa Gwamnatin Hadaka Ba


Emmerson Mnangagwa Shugaban Zimbabwe
Emmerson Mnangagwa Shugaban Zimbabwe

Yayinda aka tambayeshi ko zai kafa gwamnatin hadaka, shugaban Zimbabwe ya ce ba zai yi hakan ba saboda yana da rinjaye a majalisar kasar kuma ya yi misali da tsohon Firai Ministan Birtaniya wanda ya kafa gwamnati ba ta hadaka ba duk da cewa rinjayen mutum daya yake dashi a majalisa

Shugaban kasar Zimbabwe Emerson Mnangagwa ya fidda zaton cewa, ba zai kafagwamnatin hadin kan kasa ba duk da nasarar da ya samu a zaben da ya kawo shi kan karagar mulki da yayi ba bada wani tazara mai yawa ba

Sai dai kuma bangaren masu adawa suna haramar kalubalantar sakamakon zaben a kotu kamar yadda wakilin wannan gidan radiyon Columbus Mavhanga ya aiko da rahoto daga birnin harare.

Sailin da gidan talabijin na SKY ya tambaye shi ko zai kafa gwamnati hadin kan kasa ganin bada wata rata sosai yayi nasara ba sai Emerson yace aijamiyyar sa ta ZANU -PF keda rinjaye a majilisar dokoki. Sai ya ce

“A shekarar 1964 Harold Wilson na kasar Birtaniya yana da kujera daya tak a majilisa, kuma da kujera daya ce ya yi galaba akan yan jamiyyar masu ra’ayin yan mazan jiya ya kafa gwamnatin sa, kuma ya ,mulki kasar ta Birtaniya, to balle ni dake da kashi biyu cikin ukku na masu rinjaye kuma da wannan ne kuke cewa in samar da gwamnatin hadin kan kasa, duk da yake wannan ba wai hakan baya da kyau ba ne, amma babu bukatar hakan. Wadanda basu jefa mani kuri’a ba da wadanda suka jefa mani, duka Zimbabwen tamu ce kuma tare zamu ciyar da ita gaba.

Zamu samar da muhawara mai ma’ana, da hangen nesa da dabaru wadanda sune ginshikin tafiyar mu”.

Sai dai shugaban ‘yan adawa Chamisa yaki ya amince da sakamakon zaben da hukumar zaben kasar ta bayar, tare da zargin hukumar da yin magudi a madadin jamiyyar ZANU-PF

A satin da ya gabata sai da ‘yan adawa suka gudanar da zanga-zanga a babban birnin kasar Harare, inda ‘yan sanda suka yi anfani da hayakin nan maisa kwalla da watsa tafasasshen ruwan zafi domin tarwatsa masu zanga-zangar, sai dai duk da haka an kashe mutane 6

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG