An tsinci wani bangaren jirgin sama a gabar tekun Mozambique

Ministan Sufurin kasar Malaysia

Wani attajiri mai yawon shakatawa ya gano karafan da ake kyautata zaton na jirgin Malaysia ne da ya yi batan dabo akan hanyarsa zuwa China daga Malaysia din shekaru biyu da suka gabata

An tsinci Wasu tarkacen fararen karafa a gabar tekun kudu maso gabashin Africa, kuma tuni aka aika dasu kasar Australia, domin gwadawa agani, ko bangaren jikin jirgin nan ne na kasarMalasia mai lamba 370 da yayi batar dabo tun shekaru biyu da suka gabata.

Wannan yana daya daga cikin abin mamakin da ya taba faruwa game da hadarin jirgin sama da ya kafa tarihi.

An dai tsinci wannan tarkacen ne cikin wannan satin a kasar Mozambique, a wani wuri da hukumar sufuri na kasar Autralia ta kebe. Ministan Sufuri ne Darren Chester na kasar Australia ya shaidawa majilisar wannan batu a yau din nan.

Yanzu dai hukumar hadin gwiwa wadda aka kafa domin gudanar da binciken wannan lamari na wannan jirgin mai lamba MH370, tace zata duba wadannan takarcen karahunan domin tantance ko na jirgin ne ko kuma a’a