Binciken kasa da kasa domin gano baraguzen jirgin a kudancin tekun Indiya ya ci tura, kuma ‘yan sanda Malaysia suma sun yi bincike amma basu samo komai ba.
Sfeto Janar Khalid Abubakar yace masu bincike na bukatar karin lokaci domin neman shaidu, kuma yayi gargadin cewa fa za’a iya daukar lokaci mai tsawon gaske ana wannan bincike.
Khalid ya kara da cewa ‘yansanda na cigaba da mayar da hankulansu akan yiwuwar an sace jirgin ne, ko akwai wata kumbiya-kumbiya, ko kuma akwai mai tabun hankali a cikin jirgin.
Yanzu dai, a cewar Khalid masu bincike sun tambayoyi ga mutane har sau 170, kuma yace za’a cigaba da yin tambayoyi.