Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kasa Gano Jirgin Malaysia


Jami’an kasar Australiya sun tantance cewa jirgin Malaysiannan wanda ya bace, bai fadi a yankin kudancin tekun Indiya ba, inda aka ji alamar karar na’u’ra a watan da ya wuce.

Wannan tantancewa dai an kammalata ne yau Alhamis bayan aika wani jirgin karkashin teku a karo na karshe cikin ruwa domin binciken abubuwan dake karkashin tekun dake kudu maso yammacin gabar Australiya.

A wata sanarwa, cibiyar hadin kai domin tattara bayanai, ko Joint Agency Coordination Center a turance, tace jirgin karkashin tekun mai suna Bluefin-21 bai ga alamun baraguzen jirgin ba bayan bincika fili mai tsawo da fadin kilomita 850.

Sanarwar ta kara da cewa hukumar kula da lafiyar sufurin Australiya ta yanke hukuncin cewa yanzu ba sai an lissafa wannan yanki ba a matsayin inda ake tunanin jirgin Malaysian ya fadi.

Jirgin mai kirar kamfanin Boeing 777 na dauke ne da mutane 239 a lokacin da ya bace daga na’urar ganin jirage, ba tare da wata sanarwar matsala ba, ran 8 ga watan Maris, mintuna 30 da barin birnin Kuala Lumpur a Malaysia zuwa Beijing dake Chana.
XS
SM
MD
LG