Duk da haka hukumomin Australia da Amurka wadanda suka yi magana jiya talata a cikar wata daya da bacewar jirgin, sunce akwai bukatar a yi taka-tsan-tsan.
Suk ace masu aikin neman jirgin basu sake jin wadannan kararrakin da aka ji tunda farko ranar lahadi a wani wuri mai nisan kilomita dubu daya da dari shida daga arewa maso yammacin birnin Perth na kasar Australiyan ba, a wani wuri mai zurfin ruwa na tsawon kilomita hudu da rabi.
Babban jami’I lura da ayyukan neman jirgin dan kasar Australia yace kararrakin da na’urori suka gano tunda farko sune alamomi masu karfi da za a dogara dasau wajen neman jirgin, amma yanzu yace ba tareda jin wadannan kararrakin ba, zai yi wuya a tanatance ko tsara wurare da za a fi maida hankali akansu, kuma yanzu za a jinkirta tura jirgin ruwa maras matuki zuwa karkashin ruwa idan ba an saurari karin wadannan alamomi da aka ji tunda farko ba.