Rundunar tace mutane saba’in ne yanzu haka suka ajiye makamansu, wadansu kuma suka mika kansu ga jami’an tsaron, Sai dai wadanda aka riga aka tantance yanzu su hamsin da bakwai ne, amma sauran suma suna nan tafe.
Kwamandan rundunar sojan na operation lafiya dole, Majo janar Ibrahim Attahiru, yace mayakan sun mika kansu ne a wadansu kauyuka biyu dake karamar hukumar Gwoza, ya kuma bayyana cewa, kimanin ‘yan kungiyar Boko Haram dari bakwai sun bayyana niyarsu ta yin saranda, da ajiye makamai, amma kawo yanzu mutane hamsin da bakwai ne kawai suka ajiye makamai.
Ya bayyana cewa, gwamnatin tarayya tana da wani shiri ga mutanen da suka mika kansu da kansu da ake kira “Operation safe corridor” domin sake tsugunar da su, da koya masu sana’oi yadda zasu iya rayuwa cikin al’umma ba tare da tsangwama ba.
A cikin hira da manema labarai, mutanen da suka mika makamansu, sun bayyana cewa, sun tsaida shawarar ficewa daga kungiyar ne domin sun gane cewa, dabi’unsu ba kan hanya suke ba.
Ga cikakken rahoton da wakilin Sashen Hausa Haruna Dauda Bi’u ya aiko mana daga Maiguguri.
Your browser doesn’t support HTML5