Yanzu dai kwamandar rundunar Manjo Janar Lucky Irabor ya zama kwandan rundunar hadin gwuiwa ta kasa da da kasa dake da hedkwatarta a Ndjemina babban birnin kasar Chadi.
Manjo Janar Attahiru shi ya zama sabon kwamandar rundunar dake yaki da Boko Haram wadda take da hekwatarta a Maiduguri. An kuma kara jami'an soji 147.
Kakakin rundunar sojin Najeriya Sani Usman Kukasheka yace an yi hakan ne domin sauya dabarun yaki ne da 'yan ta'addan domin gamawa da burbudin 'yan Boko Haram.
Yana mai cewa aikin da su keyi ba wai an gamashi ba ne. Suna nan suna yi har sai sun tabbatar babu wani kakkabi na 'yan Boko Haram ko wasu 'yan ta'addaan. Yace duk da nasarorin da suka samu zasu cigaba da kare tsaron kasa kamar yadda kundun tsarin kasa ya tanadar masu.
Shugaban al'ummar Chibok na Abuja Tambiza Wadaya yace duk wani matakin kawo karshen taddanci abun maraba ne domin a samu zaman lafiya a cigaba da rayuwa kamar yadda aka saba..
Nasiru Gambo Malumfashi yace barin sojoji su dade wuri guda ka iya haifar da sabo wanda zai kawo jin tausayi ko kuma wani abu mai cutarwa. Akwai illoli da yawa shi ya sa lokaci zuwa lokaci ake canzawa sojoji wurin aiki.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani
Facebook Forum