Da yake jawabi ga manema labarai, darektan watsa labarai na rundunar Majo Janar John Enanche, ya bayyana cewa, suma ba wata babbar barazana bace, ya kuma bada tabbacin cewa, suma nan ba da dadewa ba za a shawo kansu.
Tun bayan kwace jejin Sambisa aka daina jin dakarun kasar suna kai hari kan kungiyar Boko Haram, amma a maimakon haka, sai kungiyar take kara zafafa kai hare hare..
Tsohon gwamnan mulkin soja a jihar Kano, majo janar Idris Garba mai ritaya wanda ya kasance masanin tsaro ya bayyana cewa, kungiyar bata da karfi yanzu sabili da an warwatsar da membobinta gaba daya.
A nasa bangaren Majo Janar Yakubu Usman wani babban jami’in soja a shelkwatar sojin Najeriya mai ritaya, ya bayyana cewa, kwace jejin Sambisa ba tare da an kashe Abubakar Shekau ba tamkar kashe maciji ne baka kashe kanshi ba, wanda zai iya samun karfi ya yi lahani.
Ga cikakken rahoton da wakilin Sashen Hausa Hassan Maina Kaina ya aiko daga birnin Tarayya Abuja.
Facebook Forum