An Soma Fafatawa Don Dakile Ayukkan ‘Yan Bindiga A Wasu Yankunan Arewacin Najeriya

Your browser doesn’t support HTML5

Yadda ‘Yan Bindiga Ke Karbe Iko Da Kauyuka A Sokoto

A Najeriya alamu na nuna akwai yuwuwar an soma fafatawa don dakile ayukkan ‘yan bindiga a wasu yankunan arewacin Najeriya domin mazauna yankunan sun tabbatar da ganin jami'an soji suna dannawa zuwa inda ake tunanin mafakar ‘yan bindigar ce.

Duk da yake hukuma bata ce komai akan batun ba, mazauna yankin dai sun nemi a gudanar da aiki wanda ba zai bar baya da kura ba.

Yanayin da ake ciki yanzu a wasu sassan da ke fama da ‘yan bindiga a arewa maso yammacin Najeriya ya daidaita yankunan da jama'ar su inda da yawa suka kauracewa gidajensu domin su tsira da rayukansu.

Bayan kiraye kiraye da jama'ar ke yi da kuma kokawa da wasu jagororin al'umma ke yi akwai alamun watakila mahukumta aun fara tsaurara matakan da suke dauka.

A Sakkwato dake yammacin yankin arewa mazauna yankunan gabascin jihar sun tabbatar da cewa watakila an karba kiraye kirayen su domin kuwa sun ga jami'an tsaro na shiga dazukan yankin har suna jin karar harbe harbe.

A cewar wani mazaunin yankin da ma kafin isowar sojin akwai jami'an tsaro na Jtf daga jihar zamfara dake shiga yankin suna rakiyar motocin da ke zirga zirga daga Isa zuwa shinkafi ta jihar zamfara.

Aminu S Fada, wani mazaunin yankin, shima ya ce ya ga shigar jami'an sojin.

Duk da yake wasu na ganin kawo yanzu ba'a samu labarin kashe kowa ba amma dai da sojojin da masu taimaka musu suna cikin daji sun ja daga da su da barayin.

Shugaban rundunar adalci a jihar Sakkwato Bashir Altine Guyawa wanda shima dan yankin ne ya ce akwai bukatar dagewa ga wannan fadan kada ya jawowa mutanen yankin ramuwar gayya.

Jumu'ar wannan mako dai sati ke nan da ayarin gwamnatin Najeriya ya ziyarci jihar domin yin jaje akan matafiyan da aka kona a garin na Isa, inda a zantawar da ayarin yayi da jama'ar yankin ya bayar da tabbacin cewa za'a ga sauyi cikin mako biyu, to sai dai fatar jama'a itace a magance matsalolin baki daya kada a soma ban a bari kamar yadda ya sha faruwa a wasu jihohi.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

An Soma Fafatawa Don Dakile Ayukkan ‘Yan Bindiga A Wasu Yankunan Arewacin Najeriya