Tun da farko shugaba Obama ya fada cewar a da ya so yayi anfani da haduwarsa da shugaba Duterte a wurin taron koli a Laos, don tado maganar wasu mutane sama da dubu biyu da aka yi wa kisan gilla bayan zaton masu safarar miyagun kwayoyi da kuma amfani da su da aka yi musu tun lokacin da Duterte ya hau kan karagar mulki a cikin watan Yuni.
A nasa bangare, Duterte ya kare kansa game da kashe mutanen, a bisa hujjar cewa yana biyewa bukataun wadanda suka zabeshi ne.
Kafin ya bar birnin Manila jiya Litini zauwa babban birnin Lao Vientiane sai da shugaban na Philippines ya aika kashedi ga shugaba Obama.: yace ka zama mai girmamawa. Ka daina tambayoyin ba gaira ba dalili.” A nan ne kuma yayi amfani da harshen kasarsa na Tagalog yayi batanci, inda ya kira Obama da lafazin “Dan Iska.”
Da farko Shugaba Obama bai dauki kalaman na Duterte da muhimmanci ba, yace Duterte mutum ne da ke yawan son karin magana da zolaya. Amma Obama ya kara da cewa daman an shirya haduwar tasu ne a bisa tsammanin cewa shugabanna Philippines zai kasance a cikin shirin yin tattaunawa akan abubuwa masu amfani da tsari.
Bayan wasu sa’o’i, kakakin hukumar tsaron Amurka Ned Price yace an soke wannan haduwar da aka shirya yi yau talata da shugaba Duterte, a maimakon hakan, shugaba Obama zai gana da shugaban Korea ta Kudu Park Geun-hye.