Mataimaki na musamman a ofishin mukaddashin shugaban Najeriya, Alhami Hafizu Ibrahim, ya ce dole ne sai jami’an tsaro da gwamnatin jihar Borno sunyi nazari, domin tabbatar da cewa idan har Osinbajo zai kai ziyara kamar yadda aka tsara ko ya soke.
Hedikwatar sojan Najeriya ta nemi jama’a da su kwantar da hankalinsu, a cewar Birgediya Sani Usman Kuka Sheka, tsautsayi ne ya fadawa ‘yan Boko Haram ‘din da suka kai harin, domin kuwa sojojin Najeriya sun murkushe su domin kuwa babu wani ‘dan Boko Haram da ya kai labari.
Duk da yake a baya jami’an tsaron Najeriya sun tabbatarwa da al’umma cewa anci karfin Boko Haram, sai dai kuma masana ganin har yanzu kungiyar na samun goyon baya. kuma idan har ba shawo kan al’amuran cin hanci da rashawa a Najeriya ba, zai yi wahala a ci karfin al’muran Boko Haram.
Domin karin bayani saurari rahotan Hassan Maina Kaina.
Your browser doesn’t support HTML5