Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ofishin Farfasa Osinbajo Ya Mayar da Martani Kan Zargin Nuna Bangaranci


Mukaddashin Shugaban Kasa Farfasa Yemi Osinbajo
Mukaddashin Shugaban Kasa Farfasa Yemi Osinbajo

Kwanan nan wasu suna zargin Mukaddashin Shugaban Kasa da nuna bangaranci wajen wasu nade nade da yayi lamarin da ya sa ofishinsa ya mayar da martani yana karyata zargin

Dr. Junaidu Muhammad tsohon dan siyasa a jamhuriya ta farko na cikin wadanda suke zargin shi Farfasa Osinbajo da nuna kabilanci da bangaranci a nade naden da yayi.

Tsohon dan siyasan na mai cewa Shugaba Buhari, wanda yace bai san komi a harkokin tattalin arziki ba ya ba mataimakinsa dama ya kula da fannin. Ta dalilin haka ne shi Farfasa Osinbajo ya nada yawancin masana tattalin arziki daga inda ya fito, kusan kashi casa'in na mutanen daga bangarensa suka fito.

Amma ofishin Mataimakin shugaban yayi watsi da zargin. Alhaji Hafisu Ibrahim mataimaki na musamman ga Farfasa Osinbajo yace mutane masu cecekuce da basa son zaman lafiya suke zargin domin su kawowa mataimakin shugaban kasa batanci.

Dangane da cewa a wani kwamitin mutane tara, bakwai cikinsu Yarbawa ne, Hafisu Ibrahim yace ba nadasu aka yi ba ofishin da suke rike dashi ya basu kujerun.

Akan wai Farfasa Osinbajo yana take-taken neman shugaban kasa Alhaji Ibrahim ya musanta wannan ma.Yace a tarihin Najeriya babu wanda aka baiwa dama irin damar da aka bashi. Da yana da halin karbe shugabanci da tuni an gane.

Akan rabawa abokansa 'yan arewa sukari da wasu kayan masarufi lokacin azumi, Alhaji Ibrahim yace ya san mahimmancin azumi saboda haka idan ya raba masu kaya ba siyasa ba ce.

Ga rahoton Hassan Maina Kaina da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:51 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG