'Yan bindigar da ake kyautata zaton 'yan Boko Haram ne sun kai farmaki kan Maiduguri a Jihar Borno dake arewa maso gabashin Najeriya, inda aka yi ta jin karararrakin fashe-fashe da harbe-harbe.
Fararen hula da dama dake unguwar Jiddari-Polo, ta inda mayakan na Boko Haram suka kutsa cikin garin, sun arce suka bar gidajensu.
An bayar da rahoton jin harbe-harbe babu kakkautawa daga yankin unguwar ta Jiddari-Polo har zuwa kusa da barikin Giwa.
Kakakin rundunar sojojin Najeriya, Birgediya-Janar Sani Kukasheka Usman, ya bayar da sanarwa ta kafar WhatsApp yana cewa, "wasu 'yan mutane kalilan da ake kyautata zaton 'yan Boko Haram ne sun yi kokarin kai hari kan unguwar Jiddari-Polo, amma duk sojoji sun kashe su. Komai ya lafa yanzu."
A watan Disamba, gwamnatin Najeriya ta ce a zahirance an murkushe Boko Haram, a bayan da sojoji suka fatattake su daga cikin birane da garuruwan da suka kwace, suka tura su cikin dajin Sambisa. Amma tun daga lokacin, 'yan kungiyart sun ci gaba da kai hare-hare, musamman ma na kunar-bakin-wake.
Saurari hirar Aliyu mustapha da wakilinmu Haruna Dauda
Facebook Forum