Hadakar kungiyoyin matasan arewacin Najeriya tace lokaci yayi da za'a cire mutanen Igbo daga tarayyar Najeriya domin su kafa kasar Biafra da suke nema.
Hadakar kungiyoyin ta hada da kungiyoyi da dama da suka fito daga sassa daban daban na kasar.
Alhaji Hashim Shariff shugaban daya daga cikin kungiyoyin wato ACAC yana cikin wadanda suka halarci taron inda matasan suka yi jawabi. Yana mai cewa duk girman kasuwar Aba babu mutumin arewa daya da ya mallaki ginannen kanti a kasuwar. Amma duk kasuwannin arewa kabilar Igbo ce ta mamaye su. Yace kullum arewa Igbo ya ke zagi. Saboda haka yakamata 'yan arewa su hakura da zaman tare da Igbo.
Matasan sun ce a duba tarihi. Kafin kasar ta samu man fetur arewa ke bada fiye da kaso saba'in na kasafin kudin kasar tun daga shekarar 1954 har zuwa 1970. Amma da zara an samu man fetur sai Igbo suka juya suna zagin arewa.
Shi ma Ambassador Shettima Yerima dake shugabancin daya daga cikin kungiyoyin matasan yayi karin haske. Yace babu dole a zaman aure. Igbo su koma kasarsu 'yan arewa kuma su dawo gida shi ne zai fi anfani. Yace kowa yayi tafiyarsa saboda kullum ana yiwa arewa barazana.
Kiran a raba Najeriya da matasan arewa keyi bai yiwa wasu Igbo dake zaune a arewa dadi ba. Barrister Chris shugaban 'yan kabilar Igbo dake Kaduna yana mai cewa babu wani Igbo dake zaune a arewa da ya kira a kafa kasar Biafra. Ya kira matasan suyi hakuri. Zaman lafiya suke so da kuma zama tare cikin tarayyar Najeriya.
Ga rahoton Isa Lawal Ikara da karin bayani.
Facebook Forum