Haka zalika, hamshakan attajiran Najeriya Rabiu Abdulsamad mai kamfanin BUA da takwaransa Mike Adenuga mai kamfanin sadarwa na GLO sun rasa gurabensu a jerin hamshakan attajiran da mujallar kudin ta fitar.
A cikin jerin, dandalin hamshakan attajiran nan na Forbes Daily, wanda ke bin diddigin sauye-sauye na yau da kullun ga masu hannu da shuni a duk fadin duniya, ya bayyana cewa Aliko Dangote ya koma matsayi na biyu ne a yayin da dukiyarsa ta ragu daga dala biliyan 13 da miliyan 500 a shekarar 2023 zuwa dala biliyan 9 da miliyan 500 a farkon shekarar 2024 da muka shiga.
Wani binciken mujallar Forbes ya nuna raguwar arziki mai yawa a cikin attajiran sossai.
Haka kuma, arzikin attajirin dan Najeriya, Mike Adenuga, ya kai shi matsayi na goma a cikin jerin sunayen attajiran masu arzikin na nahiyar Afrika, a yayin da Patrice Motsepe, wanda ke matsayi na goma a shekarar 2023, ya rasa matsayinsa na goma mafi arziki a shekarar 2024.
Wani sauyi mai ban mamaki a cikin jerin masu arziki na Forbes a Afirka shi ne, babu wata mace da ta sami shiga jerin sunayen goma mafi arziki a farkon shekarar nan.
Masana tattalin arziki dai na alakanta raguwar arzikin wadannan attajiran da kalubalen da tattalin arziki a fadin nahiyar ke fuskanta.
Wasu kuma na danganta raguwar arzikin attajiri Dangote da faduwar darajar Naira da sauran batutuwan da suka shafi matsin tattalin arziki.
Ga jerin sunayen mafiya arziki a nahiyar Afirka da adadin kudinsu daga mujallar Forbes:
- Johann Rupert - Dala biliyan 10.3
- Aliko Dangote - Dala Biliyan 9.5
- Nicky Oppenheimer - Dala Biliyan 8.3
- Nassef Sawiris - Dala biliyan 7.4
- Abdulsamad Rabiu - Dala Biliyan 5.9
- Nathan Kirsh - Dala biliyan 5.8
- Issad Rebrab - Dala Biliyan 4.6
- Mohamed Mansour - Dala Biliyan 3.6
- Naguib Sawiris - Dala biliyan 3.3
- Mike Adenuga - Dala Biliyan 3.1