Gwamnatin jihar Borno ta sanar da sassauta dokar hana zirga zirga a jihar daga karfe shida na safe zuwa karfe bakwai na maraice, sabanin yadda yake a da, daga karfe shida zuwa karfe goma na dare.
Kwamishinan watsa labarai na jihar Dr. Mohammed Bulama ya bayyana haka ne a wata ganawa da manema labarai inda ya bayyana irin shirye shiryen da ake yi na bukin ranar Damokaradiya a jihar.
Kwamishinan yace gwamnati tana kuma shirin gudanar da wadansu shirye shirye na tunawa da zagayowar wannan rana da ya hada da liyafa ga ‘yan siyasa, da kuma wasan kwallon kafa. domin tunawa da wannan ranar.
An dage dokar takaita zirga zirgar ne domin jama’a su sami sukunin gudanarda bukukuwan. Kwamishinan yace kananan yara kusan miliyan daya ne ke gudun hijira a Maiduguri, ya kuma ce al’ummar jihar sun hakikanta cewa gwamnatin Muhammadu Buhari zata taimaka wajen shawo kan matsalar.
Ga cikakken rahoton da wakilinmu Haruna Dauda Bi’u ya aiko mana.
Your browser doesn’t support HTML5