Wannan taro na shuwagabanni biyu tamkar rantsuwa ce kawai ta rage kafin Buhari ya fara gudanar da aikin shin a shugaban kasa, saboda an damka masa kundaye wadanda ke kunshe da duk madafun mulkin da zai amfani da su, wajen gudanar da Najeriya.
Tsohon shugaban na mulkin soja, wanda ya kada Jonathan a babban zabe da aka kammala a watan Maris din da ta gabata ya nuna gamsuwarsa da irin matakan da shugaba Jonathan ya dauka na cewa ya amince an kayar da shi a zabe, wanda yace wannan shine abu na farko wanda za’a yi la’akari da shi a Najeriya a tarihinta, domin ya kawar da tashe-tashen hankula, da fitintinu daban-daban, da zasu iya kawo halakar rayuka da dukiyoyin jama’a.
Shugaba bai barin gado Jonathan yayi amfani da wannan damar wajen gabatar da bayaninsa akan irin nasarorin da ya samu, a mulkinsa na kusan shekaru 6, inda yace an samu cigaba a fannin ilimi, da yaki da cin hanci da rashawa, da sha’anin noma, da gine-gine na muhimman ma’aikatu ko masana’antu da tsare-tsare na mulki, wanda yake ganin cewa shimfida ce mai kyau yayi wadda za’a dora akan ta.
Ga alamu babu wata tangarda ganin cewa an bada wadannan kundayen mulki, ba tare da Buhari ya nuna cewa zai manta da abubuwan da Jonathan yayi musamman cewa ya yarda an kayar da shi.
Idan ana ankare, Alhamis dinnan Jonathan ya nuna damuwarsa da fargaba, har yake cewa in za’a yi bincike, to a binciki duk gwamnatocin baya, ba wai tashi kadai ce za’a bincika ba.
Shi kuma Buhari saboda tarihinsa da alkawuran da yayi wa ‘yan Najeriya, an san mutum ne dake kyamar sace-sacen dukiyar jama’a, saboda haka babu alamar cewa zai kau da kai ya kyale a mance da abubuwan da suka faru.