Janar Gowon yace Allah ya kawo lokacin da aka yi zabe cikin zaman lafiya inda kuri'un jama'a suka yi tasiri.
Ya yabawa jama'a da yin zabe ba tare da tashin hankali ba a duk fadin kasar. Yace shugaban kasa mai barin gado ya taimaka wurin kawo zaman lafiya da yadda ya amince ya sha kaye tun kafin a fitar da sakamakon zaben. Ya amince da abun da jama'a suka zaba.
Janar Gowon yace amincewar shan kaye da Jonathan ya yi kamar abun da shi ya yi ne lokacin da aka hambare gwamnatinsa a shekarar 1975. Yace ya kira duniya da sojoji su goyi bayan Janar Murtala Muhammad wanda ya hambarar da shi saboda zaman lafiyar kasar.
Yace kodayake shi da Janar Buhari sun yi shugabancin kasar cikin rigar soja amma sukan nemi shawarar jama'a kamar fararen hula saidai zabe ne babu.
Ya kira Janar Buhari mutum mai tsare gaskiya da kwazo. Saboda haka yace har ya taba bashi wani mukami na shugabanci wanda ya fi girmansa a soja. Yace ya yadda dashi kuma ya tabbata zai iya aikin, kuma ya yi. Yace ya yadda da Janar Buhari kuma zai bashi duk irin shawarar da zai iya bashi.
Ga firarsa da Muryar Amurka.