Wakilin kungiyar hadin kan tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ECOWAS Ambasada Abdu Abari a bukin rantsar da sabon shugaban kasar Najeriya ya bayyana mihimmancin ranar Damokaradiyar Najeriya ga kasashen Afrika baki daya.
Bisa ga cewar Ambasada Abari, ba a Najeriya kadai ba, amma har kasashen waje, an yi fargaban cewa, sakamakon zaben zai iya haifar da tada zaune tsaye.
Dr Abari yace gudanar da zaben da aka yi cikin kwanciyar hankali da lumana ba nasara ce ta Najeriya kadai ba, amma dukan kasashen nahiyar Afrika musamman kungiyar hadin kan Afrika AU.
Yace Najeriya ta zama abin koyi ga sauran kasashen Afrika kasancewarta babbar kasa da ta iya gudanar da zabe cikin kwanciyar hankali , da ya zama karbabbe. Ya bayyana cewa, abinda yake da muhimmanci a mulkin damokaradiya shine ganin an kare rayuka da kaddarorin al’umma a kuma maida hankali wajen biyan muradunsu.
Ya bayyana cewa, ‘yancin al’umma shine ya kamata a maida hankali a kai a cikin harkar damokaradiya game da komi.
Ga cikakken rahoton da wakilinmuj Nasiru Adamu el-Hikaya ya aiko mana.