An Sance Dalibai 78 A Bamenda Dake Arewacin Kamaru

Ana ta jimamin sace wasu dalibai 78 tare da shugaban makarantar tasu a yankin masu fafutukar 'yan aware na arewa maso yammacin Kamaru masu magana da harshen inglishi.

Yau litinin wasu ‘yan bindiga da ba’a san ko su waye ba, sun yi garkuwa da wasu dalibai 78, da kuma shugaban makarantar Cocin Presbyterian da ke yankin ‘yan aware masu magana da harshen inglishi, a arewa maso yammacin Kasar Kamaru.

Gwamna Deben Tchoffo ya tabbatar da sace daliban 78, da kuma shugaban makarantar da ke kauyen Nkwen a Bamenda, wanda shine babban birnin yankin masu fafutukar ta ‘yan aware masu magana da harshen Inglishi.

Sai dai bayanai sun yi nuni da cewa, ba’a san wadanda suka yi garkuwa da daliban ba, kuma babu masaniya kan dalilin da ya sa suka yi garkuwa da su.