Kotun Soji ta masamman karkashin jagorancin Air Vice Marshall James, ta sami Manjo janar Ibrahim Sani, da laifuka guda biyar a cikin tuhume tuhume da ake yi masa.
Laifuffukan da kotun ta tabbatar wa janar din nada alaka da almundahana, walawala, cin Amana da sama da fadi da babakere .
Kotun ta sami manjo janar Ibrahim Sani, da laifin mallakawa kansa wani bangare na filin rundunar Sojan Najeriya mai girman Hecta dari uku da talatin da shida (336), kazalika kotun tace janar din an doramasa alhakin karbo takardun mallakar wannan fili daga mahukuntar babbar birnin tarayyar Najeriya watau Abuja, amma sai ya kasafta filin ta hanyar amfani da wani kafaninsa na boge da shi kadai ke sa hannu a ciki.
Manjo janar Ibrahim Sani, ya dai yi watandar wannan fili ne inda baya ga baiwa rundunar Sojin najeriya wani bangaren filin ya mallakawa kansa wani bangare sannan ya sayarda wasu bangarori uku akan Naira miliyan goma, na biyu akan Naira miliyan bakwai da kuma Naira miliyan shida.
Da yake zartar da hukunci shugaban kotun Air Vice Marshall James, yace bisa wannan aika aika kotun ta rage masa mukamin daga Majo janar zuwa Brigediya janar sanan zai maido da Naira miliyan ashirin da uku, na filayen da ya sayar.
Your browser doesn’t support HTML5