An Samu Sabanin Ra'ayi Game Da Yadda Za a Kawo Sauyi a Libya

Fransa da kasar Italiya suna sabanin ra'ayi game da yadda za'a kawo a sauyi a Libya, bayan kawar da gwamnatin marigayi Moammar Gaddafi.

Yanzu haka dai takaddamar ta fito a bainar jama'a cikin 'yan watannin baya bayan nan, lamari da ya sa masu nazari suke nuna fargabar zaman tankiya tsakanin sassan biyu zata yi zagon kasa ga muhimmin aiki na yaki da kungiyoyin mayakan sakai dake kasar msu alaka da ISIS.

Rahotanni daga kasar suna cewa an karya lagon da kungiyar a Libya bayan da aka tusa keyarta daga babbar tunganta a Sirte tareda taimakon hare hare da jiragen yaki da Amurka ta jagoranta, amma yanzu kungiyar ta fara farfadowa.

Matsalar ta samo asali ne kan yadda faransa ta wuce kan gaba wajen kai hare-haren bama-bamai kan Libya, wadda sauran manyan kasashen duniya suka bi bayanta, har ta kai ga hambare gwamnatin Moammar Gaddafi.

Hukumomi a Italiya kasar da ta yiwa Libya mulkin kalla, sun hakikance sosai cewa "Faransa ta kwace Libya daga hanunta. Wadda Italiyan take kallo a zaman "cin fuska."

Masana suna gani wannan takaddamar zata rarraba kwunan wakilan kungiyar tarayyar turai wajen yakin da ta'addanci a Libya.