Wasu yan bindiga sun bude wuta a wajen da ake gudanar da faretin sojoji a kudu maso yammacin Iran, akalla mutane ashirin da hudu ne suka mutu yayin da fiye da 53 suka ji rauni a cewar ma’aikatar yada labaran kasar.
Kungiyar yan ta’adda ta IS ta dauki alhakin wannan hari na yau Asabar a Ahvaz dake shiyyar Khuzestan.
Akwai banbance banbancen bayanai da suka fito sakamakon lamarin.
Jami’ai sunce an kashe yan bindiga biyu, amma kuma wasu jami’an sun ce an kama wasu biyu dake da alaka da harin.
Tashar talabijin ta kasar ta ce maharan sun kai harin ne a wani dabe da jami’an Iran suka taru don kallon faretin tunawa da ranar da aka kaddamar da yaki tsakanin jamhuriyar musuluncin na shekarar 1980 zuwa 1988 akan Iraqi, wanda an gabatar da ire iren wannan fareti a sauran wurare a fadin kasar.
Ministan harkokin wajen Iran Mohammed Javad Zarif ya dora laifin harin akan wadanda ya kira “Yan ta’addan yankin da iyayen gidansu.”
Wannan wani kalamine da Iran ke amfani dashi wajen kiran abokiyar adawar ta Saudi Arabiya da Israila.
Facebook Forum