An Samu Katsewar Wutar Lantarki A Duk Fadin Najeriya

Wutar lantarki ta katse a duk fadin kasar Najeriya

An samu katsewar wutar lantarki a duk fadin Najeriya a yau Alhamis bayan da tashar wutar lantarkin kasar ta tsaya sakamakon wata matsala da ta samu, kamar yadda kamfanonin rarraba wutar lantarki a yammacin Afirka suka ruwaito.

WASHINGTON, D. .C. - Katsewar wutar ya shafi dukkan jihohin Najeriya 36 da kuma babban birnin tarayya Abuja. Tashar wutar lantarkin ta sha lalacewa a lokuta da dama, kuma yanzu dai ba'a iya bayyana lokacin da za'a dawo da wutar lantarki ba.

Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na shiyyar Enugu (EEDC), wanda ke samar da wutar lantarki a kudu maso gabashin Najeriya, ya fitar da sanarwar cewa an samu lalacewar “tsarin gaba daya”. "Saboda wannan al’amari, jama’a ba za su samu wutar lantarki ba," in ji kakakin kamfanin Emeka Ezeh.

Irin wannan rashin wutar lantarki dai ya zama ruwan dare a Najeriya da ke fama da lalatattun kayan wutar lantarki, abin da ke haifar da katsewar wutar lantarki akai-akai.

"Za'a dawo da samar da wutar lantarki da zarar an sami gyara tashar samar da wutar lantarkin," in ji kamfanin rarraba wutar lantarki na Kaduna da ke ba da wutar lantarki ga sassan Arewacin Najeriya a cikin wata sanarwa ranar Alhamis.

-AP